THE COMPLETE HOLY QURAN HAUSA TRANSLATION | Quran Hausa translation | Quran Hausa PDF | Quran in Arabic and Hausa
Al-ƙur'ani mai Girma Fassarar Marigayi Malam Abubakar Mahmoud Gumi wanda a shekarar 1987 ya samu lambar yabo ta Sarki Faisal daga kasar Saudiyya saboda fassarar Al-Qur'ani mai girma zuwa harshen Hausa. Wannan Manhajja na aiki ba tare da data ba.
A wannan manhajja ta Alƙur'ani mai Girma zaku samu abubuwa kamar haka:
1. Cikakken karatun Al-ƙur'ani mai Girma mortar Sheikh Mahmoud Khalil Al-Hussary daga baƙara zuwa Nasi
2. Alƙurani bugon hannu na Malam Mahiru Sharif Bala Kano wanda shi wannan qur'ani akan yi masa laƙabi da Al-Qur'an Warsu irin wanda alarammomi ke amfini dashi a makarantunmu na Allo wato tsangaya
3. Al-ƙur'ani Mai Girma izufi sittin fassara da kuma wallafar marigayi malam Abubakar Mahmoud Gumi daga Harshen Larabci zuwa Harshen Hausa. Malam Abubakar Gumi ya sami lambar yabo da karramawa daga kasar Saudiyya sakamakon wannan fassara ta Al-ƙur'ani Mai Girma da yayi daga Larabci zuwa Hausa
4. Sashen fassarar Al-ƙurani Na Gumi na da tsari biyu jerin surori da kuma jerin juzu'i-juzu'i
5. Akwai kuma Al-ƙur'ani bugon madinah wasu kance dashi Al-ƙur'ani bugon misra da riwayar Hafs An Asim
6. Zaku iya canja launin rubutun Al-ƙur'ani bugon madinah zuwa fari, baqi, ja, kore ko shudi
7. Addu'o'in Alqunut daban-daban
8. Sunken Allah dari ba daya tare da sautinsu
A daure a saure Wannen manhajja domin samun amfanuwa da littafin Al-ƙur'ani Mai Tsarki duk da cewa tana da dań nauyi. Alƙurani Mai Girma wato Quran Hausa
Al-Qur'ani (Larabci: القرآن al-Qur'an), ko kuma Alƙur'ani mai girma kamar yanda akasani, shine littafin da Allah ya Saukar a harshen Annabin Rahama, wato Larabci, kuma shine littafin da Allah ya rufe saukar da duk wani Littafi Mai tsarki a bayansa.
Tarihin shigowar Musulunci a Kasar Hausa:
A game da kasar Hausa, tarihi ya nuna mana ba a shigo mana da musulunci ta hanyar karfi ba. A’a musulunci ya shigo mana ne ta hanyoyin fataucin kasuwanci da kuma matafiya na sa-kai don neman tarihin kasa da da’awa ta wa’azi da kuma hanyar kaurace-kaurace na kabilu da al’ummu daga wuri zuwa wuri kamar yadda ya gabata.
‘Yan kasuwa su ne suka fara shigowa da musulunci kasar nan (Najeriya), amma ta hanyar daidaikun mutane ne. Wasu ma suna ganin tun a farkon karni na Hijirar Manzon Allah (S.A.W) musulunci ya fara saduwa da kasar Hausa ta gefen Katsina zuwa Kano, inda matafiya na kasuwanci suke bi daga wasu kasashe na Larabawa. Su ne kuma suka shigo mana da musulunci ta wannan hanyar zuwa arewacin Nijeriya.
Sannan hanya ta biyu ita ce ta wurin matafiya don rubuta tarihin kasa kamar su Ibn Khaldun da masu wa’azi kamar su Al-Maghili. Ta wannan fuskar sun fi mai da hankalinsu ta saduwa da sarakuna da mahukunta da malamai. A wannan hanyar ta biyu sun zo ne daga baya, kuma sun samu kasar Hausa cike take da mabiya addinin musulunci musamman ma talakawa. Watau dai a takaice talakawa sun fara karbar musulunci a kasar Hausa kafin sarakunansu su karbe shi. Misali, sarkin Katsina Korau (1320-1353) shi ne ya fara karbar addinin musulunci, sai sarkin Kano Yaji (1349-1385) wanda Wangarawa suka zo a lokacinsa, suka shigar da shi addinin musulunci. Sai sarkin Zazzau wanda ya musulunta na farko cikin sarakunanta shi ne Muhammadu Rabo. A masarautar Zamfara kuwa musulunci ya fara shigowa ne shekara ta 1640 A.D. Amma an ce kasar Zamfara ta karbi musulunci kafin 1640 A.D shi ne ingatacce. Haka dai sarakunan suka rika musulunta suna karfafa Hakimai da Dagatai nasu a cikin musulunci da masu unguwanninsu har zuwa ga talakawa.
Misali, a zamfara akwai wasu malamai wadanda ake kira malamai na ‘Yan Doto. Su wadannan malamai suna kasar Zamfara tun shekaru aru-aru kafin bayyanar Shehu Usman dan Fodiyo. Wadannan malamai su ne ake kyautata zaton cewa su suka rubuta wasu shahararrun littattafai ‘yan kanana cikin Ilmin Fiqhu da Tauhidi da sauransu. Kamar littafin Qawa’idi da Rashada da Ma’anar La’ilaha illallahu Muhammadur- Rasulullahi da makamantansu.